Judges 14:3 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mahaifinsa da mahaifiyarsa suka ce, “Babu wata karɓaɓɓiyar yarinya a cikin zuriyarku ko cikin dukan mutanenmu ne? Dole ne ka tafi wajen Filistiyawa marasa kaciya ka nemi aure?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “A auro mini ita dai. Ita ta dace da ni.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا إِيَايٜىٰنْسَ سُكَ تَمْبَيٜىٰشِ «كَرَسَ يَارِنْيَرْ دَ ذَاكَ عَوْرَ عَثِكِنْ یَنْ مَاتَانْ دَنْغِنْكَ، كُواْ عَثِكِنْ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْمُ؟ دُوانْمٜىٰ ذَاكَ تَڢِے كَاعَوْرِ مَثٜىٰ دَغَ ثِكِنْ ڢِلِسْتِيَاوَا أَرْنَ مَرَسَ كَاثِيَ؟» عَمَّا شَمْشُونَ يَثٜىٰ وَبَابَنْسَ «عِتَ ثٜىٰ وَدَّ نَكٜىٰسُواْ كَاعَوْرُواْ مِنِ عِتَ؞ إِنَ سُوانْتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma iyayensa suka ce masa, “Cikin 'yan'uwanka da mutanenka duka, ba yarinyar da za ka aura daga cikin 'yan matansu, har ka tafi ka auro mace daga na Filistiyawa marasa kaciya?” Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ita ce wadda nake bukata, ka auro mini ita. Ina sonta.”