Judges 14:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
wanda ya sa hannu ya ɗebo yana tafiya yana sha. Sa’ad da ya iso wurin iyayensa, ya ba su zuman, su ma suka sha. Sai dai bai gaya musu cewa ya ɗebo zuman daga gawar zaki ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَطٜىٰبِے ظُمَنْ أَ حَنُّنْسَ، يَنَ تَڢِيَ يَنَ شَا، حَرْ يَكَيْ وُرِنْ إِيَايٜىٰنْسَ، يَبَاسُ، سُكَ كُوَ شَا؞ عَمَّا شَمْشُونَ بَيْ ڢَطَا مُسُ يَطِبَ دَغَ ثِكِنْ غَاوَرْ ذَاكِبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya ɗebo zuman a hannunsa, yana tafe yana sha, har ya isa wurin iyayensa, ya ba su, suka sha, amma bai faɗa musu daga cikin gawar zaki ya ɗebo zuman ba.