Judges 15:1 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Daga baya, a lokacin girbin alkama, Samson ya ɗauki ɗan akuya ya tafi yă ziyarci matarsa. Sai ya ce, “Zan in shiga ɗakin matata.” Amma mahaifinta ya hana shi shiga.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْ یَنْ ݣُونَكِے، أَ لُواْكَثِنْ غِرْبِنْ أَلْكَمَ، شَمْشُونَ يَتَڢِے دُواْمِنْ يَظِيَرْثِ مَاتَرْسَ، يَرِڧٜىٰ طَنْ عَكُيَرْ دَ ذَيْبَاتَ ݣَوْتَا؞ يَثٜىٰ وَبَابَنْتَ «إِنَ سُواْ إِنْ شِغَ طَاكِنْ مَاتَتَ؞» عَمَّا بَابَنْتَ بَيْ يَرْدَبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Bayan 'yan kwanaki, sai Samson ya tafi ya ziyarci matarsa, ya kai mata ɗan akuya, a lokacin girbin alkama. Ya ce wa mahaifinta, “Zan shiga wurin matata a ɗakin kwana.” Amma mahaifinta bai yardar masa ba.