Judges 15:2 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya ce wa, “Na tabbata ba ka sonta sam-sam, don haka na ba da ita ga abokinka. Ba ƙanuwarta ta fi kyau ba? Ka ɗauke ta a maimako.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْيَثٜىٰ وَ شَمْشُونَ «حَڧِيڧَ نَايِ ڟَمَّنِ بَاكَ سُوانْتَ نٜىٰ سَمْ، دُواْمِنْ حَكَ نَا بَادَ عِتَ عَوْرٜىٰ غَ أَبُواْكِنْكَ وَنْدَ يَذَمَ أَبُواْكِنْ أَنْ‌غُواْ؞ أَيْ، یَرْعُوَرْتَ ڧَرَمَرْ تأَنَانً تَمَا ڢِے مَاتَرْكَ ݣَوْ؞ مٜىٰ ذَيْ هَنَكَ كَطَوْكٜىٰتَ أَمَيْمَكُوانْ مَاتَرْكَ؟»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ta ce wa Samson, “Na yi tsammani ba ka sonta ne sam, don haka sai na ba da ita ga wanda ya yi maka abokin ango. Amma ƙanwarta ta fi ta kyau. Ina roƙonka ka ɗauki ƙanwar maimakon matarka.”