Judges 15:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Filistiyawa suka yi tambaya suka ce, “Wane ne ya yi wannan abu?” Sai aka ce musu, “Ai, Samson ne surukin mutumin Timna, domin an ba wa abokinsa matarsa.” Saboda haka Filistiyawa suka haura suka je suka ƙone ta da mahaifinta ƙurmus da wuta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ڢِلِسْتِيَاوَا كُوَ سُكَيِ تَمْبَيَ «وَ يَيِ مَنَ وَنَّنْ أَبُ؟» سَيْ عَكَثٜىٰ مُسُ «شَمْشُونَ نٜىٰ يَيِ، غَمَا مُتُمِنْ تِمْنَ بَابَنْ مَاتَرْ شَمْشُونَ يَطَوْكِ مَاتَرْسَ يَبَا وَنْدَ يَذَمَ مَسَ أَبُواْكِنْ أَنْغُواْ؞» سَيْ ڢِلِسْتِيَاوَا سُكَ تَڢِے سُكَ ڧُواْنٜىٰ مَاتَرْ دُكْ دَ غِدَنْ بَابَنْتَ ڧُرْمُسْ دَ وُتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Filistiyawa kuwa suka ce, “Wane ne ya yi mana wannan abu?” Sai aka ce, “Samson ne, surukin mutumin Timna, domin ya ɗauki matar Samson ya ba wanda ya yi masa abokin ango.” Filistiyawa kuwa suka je suka ƙone matar, ta mutu, suka kuma ƙone gidan mahaifinta.