Judges 16:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ta kuma ɗaura su da akwasha. Ta sāke yin ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka.” Ya tashi daga barcinsa ya tumɓuke akwashan tare da zaren da aka ɗaura gashin kansa da su.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دٜىٰلِلَ تَا لَلَّشٜىٰشِ يَيِ بَرْثِ؞ سَعَدَّ يَكٜىٰ بَرْثِ سَيْ تَسَاڧَ ڧُنْشِنْ غَاشِنْ كَنْسَ غُدَا بَݣَويْ حَطٜىٰ دَ ظَرٜىٰ، تَا كُوَ طَوْرَ دَ أَبِنْ سَاڧَ؞ سَيْ تَثٜىٰ مَسَ «شَمْشُونَ! غَا ڢِلِسْتِيَاوَا عَكَنْكَ!» عَمَّا دَ جِنْ حَكَ، يَڢَرْكَ دَغَ بَرْثِ يَتُمْٻُكٜىٰ أَبِنْ سَاڧَ دُكْ دَ ظَرٜىٰنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da yake barci, Delila ta saƙa tukkwayen nan bakwai da suke kansa haɗe da zare, ta buga da akwasha, sa'an nan ta ce masa, “Ga Filistiyawa a kanka, Samson!” Da ya farka daga barcin, sai ya tumɓuke akwashar, da zaren.