Judges 16:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan ta ce masa, “Yaya kake cewa kana sona alhali ba ka yarda da ni ba? Wannan shi ne sau na uku kana mai da ni wawiya kuma ba ka nuna mini asirin ƙarfinka ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ دٜىٰلِلَ تَا ٻَاتَ ڢُسْكَ تَثٜىٰمَسَ «يَيَ ذَاكَثٜىٰ كَنَ ڧَوْنَتَ، سَعَدَّ بَاكَ سُواْنَ أَ ذُوثِيَارْكَ؟ سَوْ عُكُ كٜىٰنَنْ كَمَيْدَنِ أَبِنْ بَعَ! حَرْ يَنْذُ كَاڧِ كَڢَطَا مِنِ أَسِيرِنْ دَلِيلِنْ دَ كَنَدَ ڧَرْڢِے سُواْسَيْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Delila ta ce masa, “Ƙaƙa za ka ce kana ƙaunata, alhali kuwa ba na a zuciyarka? Sau uku ke nan ka maishe ni shashasha, ba ka faɗa mini inda ƙarfin nan naka yake ba.”