Judges 16:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَڧَرْشٜىٰ، شَمْشُونَ يَڢَطَا مَتَ أَسِيرِنْسَ دُكَ، يَثٜىٰ مَتَ «بَعَتَٻَيِ مِنِ أَسْكِبَ، غَمَا نِے نَظِرِتْ نٜىٰ، وَتُواْ كٜىٰٻَٻّٜىٰ غَ اللَّهْ ، تُنْدَغَ ثِكِنْ ثِكِنْ مَامَاتَ؞ عِدَنْ عَكَ أَسْكٜىٰ غَاشِنْ كَيْنَ، تُواْ، ذَنْ رَسَ ڧَرْڢِينَ، إِنْ ذَمَ كَمَرْ كُواْوَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A ƙarshe ya faɗa mata ainihin gaskiyar, ya ce mata, “Ba a taɓa aske gashin kaina ba, gama ni keɓaɓɓe ga Ubangiji ne tun daga cikin uwata. Idan aka yi mini aski, to, ƙarfina zai rabu da ni, in zama marar ƙarfi kamar kowa.”