Judges 16:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Samson ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Sa’an nan da dukan ƙarfinsa ya tura haikali ya fāɗa a kan shugabanni da dukan mutanen da suke ciki. Ta haka ya kashe mutane da yawa fiye da yayinda yake da rai.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ «بَرِ إِنْ مُتُ دَ ڢِلِسْتِيَاوَنْ!» يَتُورَ دَ إِيَاكَرْ ڧَرْڢِنْسَ، غِدَنْ كُوَ يَڢَاطِ عَكَنْ شُوغَبَنِّنْ دَ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَسُكٜىٰ ثِكِ؞ تَهَكَ مُتَنٜىٰنْ دَ شَمْشُونَ يَكَشٜىٰ أَ مُتُوَرْسَ سُكَڢِے وَطَنْدَ يَكَشٜىٰ أَ لُواْكَثِنْ دَ يَكٜىٰدَ رَيْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
ya yi kuwwa ya ce, “Bari in mutu tare da Filistiyawa!” Ya sunkuya da iyakar ƙarfinsa. Ɗakin kuwa ya faɗa a kan shugabannin da dukan mutanen da suke a cikin ɗakin. Mutanen da Samson ya kashe a rasuwarsa sun fi waɗanda ya kashe sa'ad da yake da rai.