Judges 17:2 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
ya ce wa mahaifiyarsa, “Shekel dubu ɗaya da ɗari ɗaya na azurfa da aka ɗauka daga gare ki wanda kuma ji kin furta la’ana a kai, azurfan yana wurina; ni ne na ɗauka.” Sa’an nan mahaifiyarsa ta ce, “ Ubangiji yă albarkace ka ɗana!”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَتَرَانَ يَثٜىٰ وَمَامَرْسَ «سَعَدَّ وَنِ يَسَاثِ أَظُرْڢَا دُبُو طَيَ دَ طَرِے طَيَ دَغَ وُرِنْكِ، نَاجِ كِنْ لَعَنْتَ ٻَرَوُانْ؞ تُواْ، غَاشِ، أَظُرْڢَنْ سُنَ تَرٜىٰدَنِ، نِے نَا طَوْكَ؞» سَيْ مَامَرْسَ تَثٜىٰ «بَرِ يَهْوٜىٰهْ يَسَا مَكَ أَلْبَرْكَ، طَانَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shi ne ya ce wa mahaifiyarsa, “Sa'ad da aka sace miki tsabar azurfan nan dubu da ɗari ɗaya (1,100), kin hurta la'ana a kan ɓarayin, na kuwa ji ki. To, ga shi, azurfar na wurina, ni na ɗauka.” Sai mahaifiyarsa ta ce, “Allah ya sa maka albarka, ɗana.”