Judges 18:17 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai mutum biyar da suka leƙi asirin ƙasar suka shiga ciki suka ɗauke gunkin da aka sassaƙa, efod, sauran allolin gida da kuma gunki na zubi yayinda firist ɗin tare da mutane ɗari shida da suka yi ɗamarar yaƙi suna tsaye a bakin ƙofa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتُمْ بِيَرْ طِنَّنْ وَطَنْدَ سُكَيِ لٜىٰڧٜىٰنْ أَسِيرِ سُكَ شِغَ ثِكِ، سُكَ طَوْكِ غُنْكِنَّنْ دَ عَكَ سَسَّڧَ عَكَ شَاڢَ دَ أَظُرْڢَا دَ عٜىٰڢُوادْ نَنٜىٰمَنْ نُڢِنْ اللَّهْ دَ سَوْرَنْ غُمَكَ نَغِدَا؞ ڢِرِسْتِ طِنْ كُوَ يأَنَانً ڟَيٜىٰ عَبَاكِنْ ڧُواْڢَ تَرٜىٰدَ سُواْجُواْجِ طَرِے شِدَنَّنْ دَسُكٜىٰ أَشِرْيٜىٰ دُواْمِنْ يَاڧِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma mutum biyar ɗin nan da suka tafi leƙen asirin ƙasar suka shiga kai tsaye, suka ɗauki gunkin da aka yi da itace, da falmaran, da kan gida, da gunki na zubi. Firist ɗin kuwa ya tsaya a bakin ƙofa tare da mutum ɗari shida ɗin nan masu shirin yaƙi.