Judges 18:27 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan suka ɗauko abin da Mika ya yi, da firist nasa, suka tafi Layish, suka fāɗa wa mutanen da suke zaman lafiya, ransu kuma a kwance. Suka fāɗa musu suka kuma ƙone birninsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
بَايَنْدَ مُتَنٜىٰنْ دَنْ سُكَ طَوْكِ غُمَكَنْ دَ مِيكَ يَيِ، تَرٜىٰدَ ڢِرِسْتِ طِنْ، سَيْ سُكَ تَڢِے بِرْنِنْ لَيِشْ، عِنْدَ مُتَنٜىٰنْ سُكٜىٰ ذَمَنْسُ أَ سَكٜىٰ رَيْ عَݣُونْثٜىٰ؞ سُكَ ڢَاطَ مُسُ دَ يَاڧِ سُكَ كَكَّشٜىٰ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ، سُكَ ڧُواْنٜىٰ بِرْنِنْ ڧُرْمُسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da Danawa suka ɗauke gumakan da Mika ya yi, da firist ɗinsa, sai suka je Layish inda suka sami mutane suna zamansu a huce. Suka hallaka su, suka ƙone birnin.