Judges 18:29 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Suka sa wa birnin suna Dan, wato, sunan kakansu Dan, wanda aka haifa wa Isra’ila, ko da yake a dā ana kira birnin Layish.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سُكَ كُوَ ثَنْجَ سُونَنْ بِرْنِنْ دَغَ لَيِشْ ذُوَا دَنْ، بِسَغَ سُونَنْ كَكَنْسُ دَنْ وَنْدَ يَكٜىٰ طَنْ يَعْڧُوبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Suka sa wa birnin suna Dan, ɗan Yakubu. Kafin wannan lokaci kuwa ana kiran birnin Layish ne.