Judges 18:30 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A can mutanen Dan suka kafa wa kansu gumaka, Yonatan ɗan Gershom, ɗan Musa, da ’ya’yansa maza firistoci ne na kabilar Dan har lokacin da aka kwashe mutane zuwa bauta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ دَنْ سُكَ كَڢَ وَنَّنْ غُنْكِنْ دَ عَكَ سَسَّڧَ دُواْمِنْ عَيِ مَسَ سُجَّدَ؞ مُتُمِنْ لَوِنَّنْ، يُواْنَتَنْ طَنْ غٜىٰرْشُوامْ دَغَ ذُرِيَرْ مُوسَٰى، يَذَمَ ڢِرِسْتِ نَاسُ؞ وَنَّنْ عِيَلِ سُنْثِيغَبَدَ ذَمَنْ ڢِرِسْتُواْثِنْ ذُرِيَرْ دَنْ حَرْ لُواْكَثِنْ دَ عَكَ ݣُوشٜىٰسُ ذُوَا ڧَسَرْ بَوْتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Danawa fa suka kafa gunkin domin su yi masa sujada. Jonatan, ɗan Gershom, ɗan Musa, shi da 'ya'yansa maza, suka zama firistocin Danawa, har zuwa ranar da aka kwashe mutanen zuwa bauta.