Judges 19:22 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Yayinda suke jin wa kansu daɗi, sai waɗansu ’yan iska daga birnin suka kewaye gidan. Suna bubbuga ƙofar, suna kira tsohon da yake da gidan suna cewa, “Ka fito mana da mutumin nan a gidanka domin mu yi jima’i da shi.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سُكٜىٰجِوَ رَنْسُ دَاطِے، سَيْغَا وَطَنْسُ یَنْ إِسْكَ دَغَ ثِكِنْ غَرِنْ سُكَ كٜىٰوَيٜىٰ غِدَنْ؞ سُكَيِ تَبُبُّغَ ڧُواْڢَرْ؞ سُكَثٜىٰ وَڟُواْهُوانْ، وَتُواْ مَيْغِدَنْ «كَڢِتَرْدَ مُتُمِنَّنْدَ يَشِغَ غِدَنْكَ، دُواْمِنْ مُيِ جِمَاعِ نَمَظَا دَشِ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da suke cikin jin daɗin ci da sha, 'yan iskan da suke birnin suka zo suka kewaye gidan, suka yi ta bubbuga ƙofar, suka ce wa tsohon, “Ka fito mana da mutumin da ya zo gidanka don mu yi luɗu!”