Judges 19:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Da sassafen kashegari rana ta biyar, ya tashi zai tafi, sai mahaifin yarinyar ya ce, “Ka ɗan zauna ka shaƙata sai rana ta yi sanyi mana!” Saboda haka su biyu suka zauna suka ci abinci tare.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَ سَسَّڢٜىٰ وَشٜىٰغَرِ رَانَ تَبِيَرْ يَتَاشِ ذَيْ تَڢِے، عَمَّا بَابَنْ مَثٜىٰنْ يَثٜىٰ مَسَ «إِنَ ضُواْڧُوانْكَ، كَثِ عَبِنْثِ تُكُنَ، سَعَنً كَيِ تَڢِيَرْكَ أَنْجِمَ ثَنْ إِنْ رَانَ تَايِ سَنْيِ؞» سَيْ سُو بِيُ طِنْ سُكَ ذَوْنَ سُكَثِ عَبِنْثِ تَرٜىٰ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A rana ta biyar, sai mutumin ya tashi da wuri don ya tafi amma mahaifin macen ya ce masa, “Ka zauna ka ci abinci tukuna har rana ta yi sanyi.” Dukansu biyu suka zauna suka ci tare.