Judges 19:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da mutumin da ƙwarƙwaransa da bawansa, suka tashi don su tafi, surukinsa, mahaifin yarinyar ya ce, “Duba, rana ta kusan fāɗuwa, yamma ta riga ta yi, ka kwana a nan. Ka sāke kwana ka ji wa ranka daɗi. Kashegari da sassafe za ka iya tashi ka kama hanyarka zuwa gida.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتُمِنْ دَ مَثٜىٰنْ دَ بَاوَنْسَ سُكَتَاشِ دُواْمِنْ سُيِ تَڢِيَرْسُ، سَيْ بَابَنْتَ يَثٜىٰ «دُوبَ، لُواْكَثِ يَتَڢِے، رَانَ تَكُسَنْ ڢَاطُوَ؞ إِنَ ضُواْڧُوانْكَ كَسَاكٜىٰ ݣُونَ كَجِوَ رَنْكَ دَاطِے؞ غُواْبٜىٰ سَيْ كَتَاشِ دَ سَسَّڢٜىٰ كَكَامَ حَنْيَرْكَ ذُوَا غِدَا؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da mutumin, da ƙwarƙwararsa, da baransa sun tashi za su tafi, sai mahaifin macen kuma ya ce masa, “Ga shi, rana ta kusan faɗuwa, yamma kuwa ta yi, ina roƙonka, ka sāke kwana ka ji wa ranka da:di, sa'an nan ka yi sammako gobe ka kama hanyarka zuwa gida.”