Judges 20:31 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Mutanen Benyamin suka fito su same su aka kuma jawo su nesa da birnin. Suka fara karkashe Isra’ilawa kamar dā, har aka kashe wajen mutum talatin a filaye da kuma a hanyoyi, wadda take zuwa Betel da kuma wadda take zuwa Gibeya.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ سُواْجُواْجِنْ بِلِيَامِنُ سُكَ ڢِتُواْ دُواْمِنْ سُيِ يَاڧِ، عَكَ جَاسُ دَغَ بِرْنِنْ؞ كَمَرْ يَدَّ سُنْ سَابَايِ، سُكَ ڢَارَ كَكَّشٜىٰ وَطَنْسُ سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞ سُنْ كَشٜىٰ سُواْجُواْجِنْ إِسْرَٰٓءِيلَ وَجٜىٰنْ مُتُمْ تَلَاتِنْ أَ ڢِيلِ دَ كُمَ عَكَنْ حَنْيَرْ دَ تَبِے ذُوَا بٜىٰتٜىٰلْ دَ وَدَّ تَبِے ذُوَا غِبٜىٰيَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Mutanen Biliyaminu kuma suka fito, suka tasar musu. Aka jawo su nesa da birnin. Suka fara kashe Isra'ilawa kamar yadda suka yi a dā, suka kashe wajen mutum talatin a kan karauka wadda ta nufi Betel da wadda ta nufi Gibeya, da filaye.