Judges 21:10 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka sai taron ya umarci jarumai dubu goma sha biyu su je Yabesh Gileyad su karkashe waɗanda suke zaune a can, duk da mata da yara.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَبُواْدَ حَكَ، تَارُوانْ جَمَعَ كُوَ سُكَ عَيْكِ سُواْجُواْجِ دُبُو غُواْمَشَا بِيُ ذُوَا يَبٜىٰشْ غِلٜىٰيَدْ سُكَ عُمَرْثٜىٰسُ «كُتَڢِے كُكَكَّشٜىٰ دُكَنْ مَذَوْنَنْ يَبٜىٰشْ غِلٜىٰيَدْ دُكْ دَ مَاتَادَ يَارَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Taron jama'a kuma suka aiki jarumawansu mutum dubu goma sha biyu (12,000) zuwa Yabesh-gileyad. Suka umarce su cewa, “Ku je ku karkashe mazaunan Yabesh duka har da mata da yara.