Judges 21:23 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Haka mutanen Benyamin suka yi. Yayinda ’yan matan suke rawa, kowane mutum ya kama ɗaya ya yi gaba da ita ta zama matarsa. Sa’an nan suka komo ƙasar gādonsu suka sāke giggina garuruwan suka kuwa zauna a cikinsu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
مُتَنٜىٰنْ بِلِيَامِنُ كُوَ سُكَيِ حَكَ؞ كُواْوَنّٜىٰنْسُ يَذَاٻِ مَثٜىٰ دَغَ ثِكِنْ یَنْ مَاتَانْدَ سُكَ ڢِتُواْ ضَوَ أَ شِلُواْ يَتَڢِے دَ عِتَ تَذَمَ مَاتَرْسَ؞ سَعَنً سُكَ كُواْمَ ڢِيلِنْسُ نَغَادُواْ؞ سُكَ سَاكٜىٰ غِنَا غَرُرُوَنْسُ سُكَ ذَوْنَ عَثِكِ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Haka kuwa mutanen Biliyaminu suka yi. Suka kama budurwai gwargwadon yawansu daga cikin masu rawa. Sa'an nan suka koma zuwa yaƙin ƙasarsu ta gādo. Suka sāke gina garuruwansu, suka zauna.