Judges 21:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan suka ce, “Wace kabila ce cikin kabilan Isra’ila ba tă zo taro a gaban Ubangiji a Mizfa ba?” Sai su gane cewa babu wani daga Yabesh Gileyad da ya zo sansani don taron.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ سُكَ تَمْبَيَ ثٜىٰوَ «كُواْ أَݣَويْ وَتَ ذُرِيَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ دَ بَتَهَوْرَ ذُوَا تَارُوانْمُ أَغَبَنْ يَهْوٜىٰهْ أَ مِظْڢَ بَ؟» سَيْ سُكَ تَرَرْ بَا وَنِ دَغَ ثِكِنْ يَبٜىٰشْ غِلٜىٰيَدْ وَنْدَ يَكَسَنْثٜىٰ عَتَارُوانْ جَمَعَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan suka ce, “Wace kabila ce daga cikin kabilar Isra'ila ba ta hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba?.. Sai suka ga, ashe, ba wani daga Yabesh-gileyad da ya halarci taron.