Judges 3:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا سَعَدَّ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُكَيِ كُوكَا غَ يَهْوٜىٰهْ ، سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَبَاسُ وَنْدَ ذَيْثٜىٰثٜىٰسُ، وَتُواْ عٜىٰهُدْ طَنْ غٜىٰرَ دَغَ ذُرِيَرْ بِلِيَامِنُ، شِيكُوَ مَيْ عَيْكِ دَ حَنُّنْ هَغُ نٜىٰ؞ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُوَ سُكَ عَيْكَ وَ سَرْكِے عٜىٰغْلُوانْ نَ مُواْوَبْ دَ ݣَوْتَيْ تَهَنُّنْ عٜىٰهُدْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma sa'ad da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, ya ba su wanda zai cece su, wato Ehud, ɗan Gera daga kabilar Biliyaminu, shi kuwa bahago ne. Isra'ilawa suka aika wa Eglon Sarkin Mowab da kyautai ta hannun Ehud.