Judges 3:16 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
To, Ehud ya riga ya ƙera takobi mai kaifi biyu mai tsawo wajen kamu ɗaya da rabi, wanda ya yi ɗamara da shi a cinyarsa ta dama ƙarƙashin rigarsa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
كَاڢِنْ يَتَاشِ، سَيْ عٜىٰهُدْ يَڧٜىٰرَ وَنِ تَكُواْبِے مَيْثِ غٜىٰڢٜىٰ بِيُ، ڟَوُانْسَ كُوَ يَا كَيْ ڧَڢَا طَيَ دَ رَبِے؞ سَيْ يَطَوْرَا تَكُواْبِنْ عَثِنْيَرْسَ تَدَمَ، يَرُڢٜىٰ دَ دُواْغُوَرْ رِغَرْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai Ehud ya ƙera wa kansa takobi mai kaifi biyu, tsawonsa kamu guda. Ya yi ɗamara da shi wajen cinyarsa ta dama a ƙarƙashin tufafinsa.