Judges 3:28 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya umarce su ya ce, “Ku bi ni, gama Ubangiji ya ba Mowab abokin gābanku a hannunku.” Haka suka gangaro tare da shi suna mallaki mashigin Urdun da ta shiga zuwa Mowab, ba su yarda wani ya haye ba.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَثٜىٰ مُسُ «كُبِيُواْ نِے! غَمَا يَهْوٜىٰهْ يَا بَادَ أَبُواْكَنْ غَابَنْكُ مُواْوَبَاوَا أَ حَنُّنْكُ؞» سَيْ سُكَ غَنْغَرَ تَرٜىٰ دَشِ، سُكَ ڨُوثٜىٰ وُرَارٜىٰنْ دَ مُواْوَبَاوَا سُكٜىٰبِے سُڧٜىٰتَرٜىٰ كُواْغِنْ يُواْدَنْ؞ بَسُبَرْ وَنِ يَڧٜىٰتَرٜىٰبَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sai ya ce musu, “Ku biyo ni, gama Ubangiji ya ba da Mowabawa maƙiyanku a gare ku.” Suka gangara, suna biye da shi. Suka ƙwace wa Mowabawa mashigan Urdun, suka hana kowa wucewa.