Judges 3:8 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Fushin Ubangiji kuwa ya yi ƙuna a kan Isra’ila har ya sayar da su ga Kushan-Rishatayim sarkin Aram-Naharayim, a wurinsa ne Isra’ilawa suka zama bayi shekara takwas.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُواْمِنْ حَكَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ ڢُشِے دَ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ سُواْسَيْ، يَبَاشٜىٰسُ أَ حَنُّنْ سَرْكِے كُشَنْ رِشَتَيِمْ نَ مٜىٰسُواْڢُواْتَمِيَ؞ مُتَنٜىٰنْ إِسْرَٰٓءِيلَ كُوَ سُكَ بَوْتَا مَسَ شٜىٰكَرَا تَݣُوسْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Domin haka Ubangiji ya husata ƙwarai da Isra'ilawa, sai ya bashe su ga Kushan-rishatayim, Sarkin Mesofotamiya. Jama'ar Isra'ila kuwa suka bauta masa shekara takwas.