Judges 4:21 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Yayel, matar Heber, ta ɗauki turken tenti da guduma ta tafi wurinsa da sauri sa’ad da yake barci saboda gajiya. Ta kafa masa turken a gindin kunnensa ta haɗa shi da ƙasa, har ya mutu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سِسٜىٰرَ كُوَ يَغَجِ سُواْسَيْ، بَرْثِ مَيْ نَوْيِ يَكَامَ شِ؞ سَيْ يَيٜىٰلْ مَاتَرْ هٜىٰبٜىٰرْ تَطَوْكِ غُدُمَ دَ ڧُوسَرْ كَڢَ تٜىٰنْتِ، تَجٜىٰ وُرِنْسَ أَ حَنْكَلِ، تَكَڢَ مَسَ ڧُوسَرْ عَكَنْسَ، ڧُوسَرْ تَبِے تَثِكِنْ كَنْسَ حَرْ تَوُثٜىٰ ثِكِنْ ڧَسَا، سَيْ سِسٜىٰرَ يَمُتُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma Yayel, matar Eber, ta ɗauki turken alfarwa da guduma, ta yi sanɗa zuwa wurinsa, ta kafa masa turken a gindin kunne, ya zarce har ƙasa, a sa'ad da yake sharar barcin gajiya. Ya kuwa mutu.