Judges 5:14 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Waɗansu suka zo daga Efraim, waɗanda ainihinsu daga Amalek ne; Benyamin yana tare da mutanen da suka bi ka. Daga Makir, shugabannin sojoji suka gangaro, daga Zebulun waɗanda suke riƙe da sandan komanda suka fito.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ إِڢْرَيِمْ سُكَ غَنْغَرُواْ ذُوَا ݣُورِ، تَرٜىٰدَ ذُرِيَرْ بِلِيَامِنُ دَ مُتَنٜىٰنْتَ؞ دَغَ مَكِرْ شُوغَبَنِّنْ سُواْجُواْجِ سُكَ غَنْغَرُواْ، مَنْيَنْ سُواْجُواْجِ سُكَذُواْ دَغَ ظٜىٰبُلُنْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Daga Ifrraimu mutane suka gangaro zuwa kwari, Bayan kabilar Biliyaminu da mutanenta. Daga Makir shugabannin sojoji suka zo, Daga Zabaluna kuma jarumawa suka gangaro.