Judges 6:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Gideyon ya shiga ciki, ya gyara ’yar akuya ya dafa, da garin efa ya yi burodi marar yisti. Da ya sa naman a kwando, romon kuma a tukunya, sai ya fito da su waje ya miƙa masa su a ƙarƙashin itacen oak.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ جِدْعَوْنَ يَتَڢِے غِدَا، يَيَنْكَ طَنْ عَكُيَ، يَدَڢَ؞ يَكُمَ طَوْكِ كِلُواْ غُواْمَ نَغَارِنْ حَڟِ، يَغَسَ غُرَاسَرْ مَرَرْ يِسْتِ دَشِ؞ يَسَا نَامَنْ عَݣُونْدُواْ، رُواْمُوانْ كُمَ يَظُبَ عَثِكِنْ تُكُنْيَ، يَذُواْ يَمِيڧَوَ مَلاَىِٕكَنْ يَهْوٜىٰهْ أَغِنْدِنْ إِتَاثٜىٰ مَرَرْ بُوشٜىٰوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak.