Judges 6:39 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’an nan Gideyon ya ce wa Allah, “Kada ka yi fushi da ni. Bari in ƙara yin wani gwaji kuma da ulun. A wannan lokaci ka sa ulun yă bushe, ƙasar kuma ta rufu da raɓa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ جِدْعَوْنَ يَثٜىٰ وَ اللَّهْ «كَدَ كَيِ ڢُشِے دَنِے، بَرِ إِنْ ڧَارَ يِنْ مَغَنَ سَوْ طَيَ تَكْ؞ إِنَ ضُواْڧُوانْكَ، بَرِ إِنْ ڧَارَ يِنْ وَنِ ڠُوجِ كُمَ دَ ڢَتَرْ نَنْ؞ أَوَنَّنْ لُواْكَثِ كَسَا ڢَتَرْ تَبُوشٜىٰ، عَمَّا ڧَسَرْ تَجِڧٜىٰ دَ رَٻَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gidiyon kuma ya ce wa Allah, “Ina roƙonka, kada ka yi fushi da ni, bari in ƙara magana sau ɗaya kurum, wato in sāke yin gwaji da ulun. Ina roƙonka ka sa a yi raɓa a ƙasa, amma kada ta taɓa ulun.”