Judges 7:13 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gideyon ya iso daidai wani yana faɗa wa wani aboki mafarkinsa, yana cewa, “Na yi mafarki, na ga dunƙule burodin sha’ir ya fāɗo a tsakiyar sansanin Midiyawa. Ya bugi tentin da ƙarfin da ya sa tenti ta kife a ƙasa.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ جِدْعَوْنَ يَ إِسُواْ، سَيْ يَجِ وَنِ مُتُمِنْ مَدْيَنَ يَنَ ڢَطَا وَ أَبُواْكِنْسَ مَڢَرْكِنْ دَ يَيِ؞ يَنَ ثٜىٰوَ «نَيِ مَڢَرْكِ؞ نَغَ دُنْڧُلٜىٰنْ غُرَاسَرْ بَلٜىٰ يَغَنْغَرُواْ حَرْ عَثِكِنْ سَنْسَنِنْمُ، يَبُغِ تٜىٰنْتِ؞ تٜىٰنْتِنْ كُوَ يَڢَاطِ يَݣُونْتَ عَڧَسَا غَبَاطَيَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'ad da Gidiyon ya tafi, sai ya ji wani yana faɗa wa abokinsa mafarkin da ya yi. Ya ce, “Na yi mafarki, na ga wainar sha'ir ta faɗo a tsakiyar sansaninmu. Ta zo ta bugi alfarwa. Alfarwar kuwa ta fāɗi rigingine.”