Judges 7:19 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gideyon da mutum ɗari da suke tare da shi suka kai sansanin da tsakar dare bayan an sauya matsara. Suka busa ƙahoninsu, suka farfashe tulunansu da suke hannuwansu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
جِدْعَوْنَ تَرٜىٰدَ مُتُمْ طَرِے وَطَنْدَ سُكٜىٰ تَرٜىٰدَشِ، سُكَ كَيْ بَاكِنْ سَنْسَنِنْ وَجٜىٰنْ ڟَكَرْ دَرٜىٰ بَايَنْدَ عَكَ ثَنْجَ مَاسُ غَادِ؞ سَيْ سُكَ بُوسَ ڧَهُواْنِ، سُكَ كُمَ ڢَرْڢَسَ تُلُنَنْ دَسُكٜىٰ أَ حَنُّوَنْسُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gidiyon da mutum ɗari da suke tare da shi, suka kai gefen sansanin wajen tsakiyar dare, bayan an sauya matsara. Sai suka busa ƙahonin, suka fasa tulunan da suke a hannuwansu.