Judges 7:22 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sa’ad da aka busa ƙahonin nan ɗari uku sai Ubangiji ya sa Midiyawa suka yi ta saran juna. Mayaƙan suka gudu zuwa Bet-Shitta wajen Zerera har zuwa yankin Abel-Mehola kusa da Tabbat.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَدَّ مُتَنٜىٰنْ جِدْعَوْنَ سُكَ بُوسَ ڧَهُواْنِ طَرِے عُكُنَّنْ، سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَرِكِتَرْدَ سُواْجُواْجِنْ مَدْيَنَ سُكَيِ تَسَسَّارٜىٰ جُونَنْسُ دَ تَكُبَ؞ سُكَ غُدُ ذُوَا بٜىٰتْ شِتَّ تَوَجٜىٰنْ ظَرٜىٰتَنْ، حَرْ كُمَ ذُوَا غَرِنْ أَبٜىٰلْ مٜىٰهُواْلَ، كُسَدَ تَبَّتْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Da suka busa ƙahonin nan ɗari uku, sai Ubangiji ya sa Madayanawa suka yi ta sassare junansu da takuba. Suka gudu zuwa Zerera har Bet-shitta, har kuma zuwa garin Abel-mehola, kusa da Tabbat.