Judges 7:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma Ubangiji ya ce wa Gideyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai cikin ruwa, in kuma tankaɗe maka su a can. In na ce, ‘Wannan zai tafi da kai,’ to, zai tafi; amma in na ce, ‘Wannan ba zai tafi da kai ba,’ to, ba zai tafi ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ يَهْوٜىٰهْ يَثٜىٰ وَ جِدْعَوْنَ «حَرْ يَنْذُ مُتَنٜىٰنْ سُنْيِيَوَ؞ كَيْسُ بَاكِنْ كُواْغِ دُواْمِنْ إِنْ وَارٜىٰ مَكَسُ عَثَنْ؞ سَعَدَّ نَثٜىٰ، ‹غَا وَنْدَ ذَيْ تَڢِے تَرٜىٰدَكَيْ،› شِينٜىٰ ذَيْ تَڢِے، وَنْدَ كُمَ نَثٜىٰ، ‹بَذَيْ تَڢِے تَرٜىٰدَكَيْ بَ،› شِيكُوَ بَذَيْ تَڢِے تَرٜىٰدَكَيْ بَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ubangiji ya ce wa Gidiyon, “Har yanzu mutanen sun yi yawa. Ka kai su bakin rafi domin in jarraba maka su a can. Wanda na faɗa maka shi zai tafi tare da kai, to, shi ne zai tafi, wanda kuma na faɗa ba zai tafi tare da kai ba, to, ba zai tafi ba.”