Judges 8:19 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Gideyon ya ce, “Waɗannan ’yan’uwana ne, ’ya’yan mahaifiyata. Muddin Ubangiji yana a raye, da a ce kun bar su da rai, da ba zan kashe ku ba.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
جِدْعَوْنَ يَأَمْسَ يَثٜىٰ «سُو یَنْعُوَنَنٜىٰ، مَامَرْمُ طَيَ؞ نَا ضَنْڟٜىٰ مُكُ دَ سُونَنْ يَهْوٜىٰهْ مَيْ رَيْ دَبَدُواْمِنْ كُنْ كَشٜىٰسُبَ دَ بَذَنْ كَشٜىٰكُبَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Gidiyon ya ce musu, “Su 'yan'uwana ne, mahaifiyarmu ɗaya. Da ba ku kashe su ba, da ba zan kashe ku ba.”