Judges 9:24 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Allah ya yi haka saboda kisan ’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan ’yan’uwansa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
وَنَّنْ يَڢَرُ نٜىٰ دُواْمِنْ أَ رَامَ كَشٜىٰوَرْ یَیَ سَبَعِنْ نَ يٜىٰرُبَّعَلْ، كُمَ أَلْحَكِنْ جِنِنْسُ يَكَسَنْثٜىٰ عَكَنْ أَبِمٜىٰلٜىٰكْ دَ كُمَ عَكَنْ شُوغَبَنِّنْ شٜىٰكٜىٰمْ وَطَنْدَ سُكَ تَيْمَكٜىٰشِ يَكَشٜىٰ یَنْعُوَنْسَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Wannan ya faru domin a ɗauki fansar jinin, 'ya'yan Yerubba'al, maza, su saba'in, a kan Abimelek ɗan'uwansu, wanda ya kashe su, da kuma a kan shugabannin Shekem, waɗanda suka taimake shi ya kashe 'yan'uwansa.