Judges 9:25 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cikin hamayya da shi waɗannan ’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
شُوغَبَنِّنْ شٜىٰكٜىٰمْ، سَبُواْدَ سُنَ غَابَادَ أَبِمٜىٰلٜىٰكْ، سُكَسَا مُتَنٜىٰ سُيِ ݣُونْتُوانْ ٻَوْنَ عَثِكِنْ دُوَڟُو؞ سُكَ يِتَيِ وَدُكْ وَنْدَ يَبِے تَوَنَّنْ حَنْيَ ڢَشِ؞ عَكَ كُوَ ڢَطَا وَ أَبِمٜىٰلٜىٰكْ أَبِنْدَ يَكٜىٰ ڢَرُوَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Shugabannin Shekem kuwa suka sa mutane su yi kwanto a kan dutwatsu gāba da Abimelek. Suka yi wa duk wanda ya bi ta wannan hanya fashi. Sai aka faɗa wa Abimelek.