Judges 9:33 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Kashegari da safe, sai ku tashi ku fāɗa wa birnin. Sa’ad da Ga’al da mutanensa suka faɗa maka, sai ka yi abin da ka iya yi da su.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَعَنً غُواْبٜىٰ دَ سَڢٜىٰ دَ ڢِتُواْوَرْ رَانَ، كَتَاشِ كَڢَاطَوَ بِرْنِنْ دَ يَاڧِ بَاڟَمَّنِ؞ لُواْكَثِنْ دَ غَعَلْ دَ مُتَنٜىٰنْسَ سُكَ ڢِتُواْ دُواْمِنْ سُيَاڧٜىٰكَ، سَيْ كَبُغٜىٰسُ يَدَّ كَاعِيَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”