Judges 9:49 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Saboda haka mutanen suka sassare rassan itatuwa suka bi Abimelek. Suka tattara su a jikin mafakar suka kuma cinna mata wuta a kan mutanen da suke a ciki. Ta haka dukan mutanen da suke cikin hasumiyar Shekem, wajen maza da mata dubu ɗaya suka mutu.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ كُواْوَنٜىٰ مُتُمْ يَجٜىٰ يَسَارٜىٰ رٜىٰشٜىٰنْ إِتَاثٜىٰ؞ سَعَنً سُكَبِے أَبِمٜىٰلٜىٰكْ سُكَ تَارَ عِتَتُوَنْ أَجِكِنْ وُرِنْ ٻُيَ أَغِدَنْ غُنْكِنْ؞ سُكَسَا وُتَا عَكَنْ غِنِنْ تَرٜىٰدَ مُتَنٜىٰنْ عَثِكِ؞ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ دَ سُكَ تَارُ عَثِكِنْ وُرِنْ ٻُيَنَّنْ أَ شٜىٰكٜىٰمْ سُكَ مُتُ غَبَاطَيَ، وَجٜىٰنْ مُتُمْ دُبُو طَيَ مَظَا دَ مَاتَا؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Kowane mutum kuwa ya sari reshen itace, ya bi Abimelek. Suka tara rassan a jikin hasumiyar. Suka sa wa hasumiyar wuta, duk da mutanen da suke cikinta. Ta haka dukan mutanen hasumiyar Shekem suka mutu, mata da maza, wajen mutum dubu.