Judges 9:51 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A cikin birnin, akwai wata hasumiya mai ƙarfi, inda dukan maza da mata, dukan mutanen birnin, suka ɓuya. Suka kulle kansu, suka kuma hau rufin hasumiyar.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَثِكِنْ بِرْنِ أَݣَويْ وَتَ حَصُومِيَا مَيْ ڧَرْڢِنْ غَسْكٜىٰ؞ سَيْ دُكَنْ مُتَنٜىٰنْ غَرِنْ مَظَا دَ مَاتَا حَرْ مَا دَ شُوغَبَنِّنْ، سُكَ غُدُ سُكَ شِغَ ثِكِ؞ سُكَ كُلّٜىٰ كَنْسُ عَثِكِ، سُكَ هَوْرَ كَنْ رُڢِنْ حَصُومِيَرْ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar.