Lamentations 1:18 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“ Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
أَبِنْ دَ يَهْوٜىٰهْ يَيِ دَيْدَيْنٜىٰ، غَمَا نِے نَا يِتَاوَيٜىٰ غَ مَغَنَرْسَ؞ كُجِ، يَا كُو ڧَبِيلُ دُكَ، دُوبِے وَهَلَاتَ! بُدُرْوَيْنَ دَ سَمَارِنَ، أَنْ كَيْسُ بَوْتَا!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Abin da Ubangiji ya yi daidai ne, Gama ni na ƙi bin maganarsa, Ku ji, ya ku jama'a duka, Ku dubi wahalata, 'Yan matana da samarina, An kai su bauta!