Lamentations 1:7 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
A cikin kwanakin da take shan wahala take kuma yawo Urushalima ta tuna da dukan dukiyar da take da ita a kwanakin dā can. Sa’ad da mutanenta suka faɗa cikin hannun abokan gābanta, ba wanda ya taimake ta. Maƙiyanta suka dube ta suka yi mata dariya don hallakar da ta auko mata.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَݣُونَكِنْ عَذَابَرْتَ دَ رَشِنْ وُرِنْ ذَمَنْتَ، عُرُوشَلِيمَ تَتُنَ دَ رَايُوَرْتَ تَدَرَجَ تَدَا؞ أَ لُواْكَثِنْ دَ تَڢَاطَ أَ حَنُّنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْتَ، كُمَ بَابُ مَيْ تَيْمَكُوانْتَ، سَيْ أَبُواْكَنْ غَابَنْتَ سُكَيِ مَتَ كَلُّوانْ رٜىٰنِ سَبُواْدَ ڢَاطُوَرْتَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama, Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā. A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi, Ba wanda ya taimake ta, Maƙiyanta sun gan ta, Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.