Lamentations 1:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
جِنِنْ ڧَظَنْتَرْتَ يَنُونَ أَ ذَنٜىٰنْتَ، بَتَمَا يِتُنَانِ يَدَّ ڧَرْشٜىٰنْتَ ذَيْ كَسَنْثٜىٰبَ؞ غَاشِ، ڢَاطُوَرْتَ تَذَمَ مُومُّنَ، بَابُ مَيْ تَعَظَنْتَرْ دَ عِتَ؞ يَا يَهْوٜىٰهْ ، دُوبِے وَهَلَاتَ! أَبُواْكَنْ غَابَنَ سُنْثِ نَصَرَا عَكَيْنَ!
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ƙazantarta tana cikin tufafinta, Ba ta tuna da ƙarshenta ba, Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce, Ba ta da mai yi mata ta'aziyya. “Ya Ubangiji, ka dubi wahalata, Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”