Lamentations 2:16 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Maƙiyanki duka suna ta surutu game da ke; suna tsaki suna cizon haƙora suna cewa, “Mun hallaka ta. Wannan ce ranar da muke jira; yau mun gan ta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دُكَنْ أَبُواْكَنْ غَابَنْكِ سُنْ بُوطٜىٰ بَاكِنْسُ كَمَرْ ذَاكُواْكِ سُنَ غَابَادَكٜىٰ، سُنَ ڟَكِ، سُنَ ثِظُوانْ هَڧُواْرَ، سُنَ ثٜىٰوَ «أَيْ، مُنْ هَلَكَاتَ! رَانَثٜىٰ وَدَّ مُكٜىٰ جِرَا، غَاشِ كُوَ، تَذُواْ، مُنْ غَنْتَ!»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Maƙiyanki duka sun wage bakinsu gāba da ke, Suna tsāki, suna cizon bakinsu, Suna ihu, suna cewa, “Mun hallaka ta! Ai, wannan ita ce ranar da muke fata! Ga shi kuwa, ta zo, mun gan ta!”