Lamentations 2:6 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Ya rushe haikalinsa kamar lambu; ya hallaka wurin yi masa sujada. Ubangiji ya sa Sihiyona ta manta da bukukkuwanta da kuma ranakunta na Asabbaci; a cikin zafin fushinsa ya watsar da sarki da firist.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
يَرُشٜىٰ هَيْكَلِنْسَ كَمَرْ بُكَّ أَغُواْنَ، يَكَوَرْدَ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَرْسَ؞ أَ سِهِيُواْنَ يَهْوٜىٰهْ يَكَوَرْدَ بُكُكُوَ دَ كِيَايٜىٰوَرْ رَانَرْ هُوتُ تَمَكُواْ؞ أَ ذَاڢِنْ ڢُشِنْسَ يَڧِ سَرْكِے دَ ڢِرِسْتُواْثِے؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Ya rushe Haikalinsa kamar bukka cikin gona, Ya mai da wurin yin ƙayyadaddun idodinsa kufai. Ubangiji ya sa ƙayyadadden idi da kiyaye Asabar Su ƙare a Sihiyona, Da zafin fushinsa kuma ya wofinta sarki da firist.