Leviticus 1:9 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Zai wanke kayan cikin da kuma ƙafafun da ruwa, firist ɗin kuwa zai ƙone dukan waɗannan a kan bagade. Hadaya ce ta ƙonawa, hadaya ce kuma wadda aka yi da wuta, mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ذَاعَ وَنْكٜىٰ كَايَنْ ثِكِنْ دَ ڧَڢَاڢُنْ دَبَّرْ دَ ضُوَ؞ سَيْ ڢِرِسْتِ يَڧُواْنَسُ دُكَ عَكَنْ بَغَدٜىٰنْ هَدَايَ تَڧُواْنَاوَا، هَدَايَرْدَ عَكَ مِيڧَ دَ وُتَا، مَيْ دَاطِنْ ڧَنْشِ غَ يَهْوٜىٰهْ ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma mai hadayar zai wanke kayan ciki da ƙafafu da ruwa, sa'an nan firist ya ƙone duka a kan bagaden, hadaya ce ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji.