Leviticus 10:14 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Amma kai da ’ya’yanka maza da mata za su iya ci ƙirjin da aka kaɗa, da kuma cinyar da aka miƙa. Ku ci su a wuri mai tsabta; an ba da su gare ku da kuma ’ya’yanku a matsayin rabo daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
عَمَّا ڧِرْجِ دَ ثِنْيَ وَطَنْدَ عَكَ مِيڧَ هَدَايَ تَطَغَوَ ذَاكُثِ دَكَيْ دَ یَیَنْكَ مَظَا دَ مَاتَا أَوُرِے مَرَرْ ڧَظَنْتَا؞ غَمَا أَنْبَاكُسُ، كَيْ دَ یَیَنْكَ، سُذَمَ رَبُوانْكُ دَغَ ثِكِنْ هَدَايُ نَڠَرَنْ زُمُنْثِ نَجَمَعَرْ إِسْرَٰٓءِيلَ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Amma ƙirjin da aka yi hadayar ta kaɗawa da shi da cinyar da aka miƙa, za ka ci su a kowane tsabtataccen wuri, da kai da 'ya'yanka mata da maza, gama wannan ne rabon da aka ba ku, daga hadayun salama na Isra'ilwa.