Leviticus 10:15 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Cinyar da aka miƙa da kuma ƙirjin da aka kaɗa, dole a kawo su tare da ɓangarori kitsen hadayun da aka yi ta wuri wuta, don a kaɗa a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa. Wannan zai zama na kullayaumi gare ka da ’ya’yanka, yadda Ubangiji ya umarta.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
ثِنْيَ دَ ڧِرْجِ وَطَنْدَ عَكَمِيڧَ هَدَايَ تَطَغَوَ غَ يَهْوٜىٰهْ ، تَرٜىٰدَ كِڟٜىٰنْ هَدَايُنْ دَ عَكَ ڧُواْنٜىٰ دَ وُتَا ذَاسُ ذَمَ رَبُوانْكُ دَكَيْ دَ یَیَنْكَ حَرْ أَبَدَا، بِسَغَ يَدَّ يَهْوٜىٰهْ يَعُمَرْتَ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Za su kawo cinyar hadayar ɗagawa da ƙirjin hadayar kaɗawa tare da kitsen hadayun ƙonawa domin a yi hadaya ta kaɗawa ga Ubangiji. Wannan zai zama rabonka da na 'ya'yanka har abada kamar yadda Ubangiji ya umarta.”