Leviticus 10:4 — Compare Translations

3 translations compared side by side

Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Sai Musa ya kira Mishayel da Elzafan, ’ya’yan Uzziyel kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan; ku ɗauki ’yan’uwanku waje da sansani, daga gaban wuri mai tsarki.”
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
سَيْ مُوسَٰى يَكِرَا مِشَيٜىٰلْ دَ عٜىٰلْظَڢَنْ، یَیَ مَظَا نَ عُظِّيٜىٰلْ طَنْعُوَنْ بَابَنْ هَٰرُونَ؞ يَثٜىٰ مُسُ «كُذُواْ كُسَ كُݣُوشِ غَوَوَّكِنْ یَنْعُوَنْكُ دَغَ تٜىٰنْتِنْ ذُوَا بَايَنْ ذَنْ‌غُواْ؞»
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Musa ya kirawo Mishayel da Elzafan 'ya'ya maza na Uzziyel, kawun Haruna, ya ce musu, “Ku zo nan, ku ɗauki gawawwakin 'yan'uwanku daga gaban wuri mai tsarki zuwa bayan zango.”