Leviticus 10:9 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
“Kai da ’ya’yanka maza, ba za ku sha ruwan inabi ko wani abu mai sa jiri ba a duk sa’ad da za ku shiga cikin Tentin Sujada, in ba haka ba za ku mutu. Wannan dawwammamiyar farilla ce wa tsararraki masu zuwa.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
«كَيْ دَ یَیَنْكَ مَظَا، بَذَاكُشَا ضُوً إِنَبِے كُواْ وَنِ أَبُ مَيْسَا بُغُوَ بَ، دُكْ سَعَدَّ ذَاكُ شِغَ تٜىٰنْتِنْ سَدُوَ، دُواْمِنْ كَدَ كُمُتُ؞ وَنَّنْ ڧَٰعِدَ ثٜىٰ تَدِنْدِنْدِنْ دَغَ نَنْ حَرْ إِيَاكَرْ ڟَارَرَّكِنْكُ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
“Kada kai da 'ya'yanka maza ku sha ruwan inabi, ko abin sha mai ƙarfi sa'ad da za ku shiga alfarwa ta sujada don kada ku mutu. Wannan doka ce a dukan zamananku.