Leviticus 11:27 — Compare Translations
3 translations compared side by side
Hausa (Sabon Rai Don Kowa 2020)
Duk abin da yake tafiya a kan dāginsa cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa yamma.
Hausa Arabic 2020 (أَتَّوْرَتْ دَ أَنَّبَاوَا)
دَغَ ثِكِنْ دَبُّواْبِنْ دَسُكٜىٰ تَڢِيَ دَ ڧَڢَا حُطُ، مَاسُ تَڢِنْ ڧَڢَا إِرِنَّݣَنْوَ ذَاسُ ذَمَ مُكُ أَبِنْ ڧَظَنْتَا؞ دُكْ كُمَ وَنْدَ يَتَٻَ مُوشٜىٰنْسُ ذَيْ ڧَظَنْتُ حَرْ يَمَّ؞
Hausa Bible 1979 (Littafi Mai Tsarki)
Duk abin da yake tafiya a kan daginsa daga cikin dabbobin da suke da ƙafa huɗu, haram ne a gare ku. Duk wanda ya taɓa mushensu zai ƙazantu har zuwa maraice.